Ez 27:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sun yi matuƙan jirgin ruwanki da katakon itacen oak na Bashan.Sun daɓe jirgin ruwanki da itacen kasharina na bakin tekun Kittim,Sa'an nan sun manne masa hauren giwa.

7. An yi filafilan jirgin ruwanki da lilin mai kyau, mai ado daga Masar,Don ya zama alama.An yi tutar jirgin ruwanki da shuɗi da shunayya na gaɓar tekun Elisha.

8. Mazaunan Sidon da Arwad su ne matuƙa,Masu hikima, waɗanda suke cikinki, su ne jagora.

9. Dattawan Gebal da masu hikimarta suna tare da ke,Suna tattoshe mahaɗan katakon jirginki,Dukan matuƙan jiragen ruwa sun zo wurinki don kasuwanci.

10. “ ‘Mutanen Farisa, da na Lud, da na Fut suna cikin sojojinki don su yi miki yaƙi. Sun rataya garkuwoyi, da kwalkwali a cikinki. Sun samo miki daraja.

11. Mutanen Arward sun kewaye kan garunki. Mutanen Gamad kuma suna tsaron hasumiyarki. Sun rataya garkuwoyinsu a jikin garunki. Sun ƙawata ki ƙwarai.

12. “‘Tarshish abokiyar cinikinki ce, saboda yawan dukiyarki ta sayi kayan cinikinki da azurfa, da baƙin ƙarfe, da kuza, da darma.

13. Mutanen Yawan, da na Tubal, da na Meshek, abokan kasuwancinki, sun sayi kayan cinikinki da mutane da tasoshin tagulla.

14. Mutanen Togarma kuma sun sayi kayan cinikinki da dawakai da dawakan yaƙi, da alfadarai.

15. Mutane Dedan abokan cinikinki ne. Kasashe da yawa kuma na gaɓar teku sun zama kasuwarki. Sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya.

16. Suriya kuma abokiyar cinikinki ce saboda yawan kayan cinikinki. Sun sayi kayan cinikinki, da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.

17. Mutanen Yahuza da na ƙasar Isra'ila abokan cinikinki ne. Sun sayi kayan cinikinki da alkama, da zaitun, da 'ya'yan ɓaure, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.

Ez 27