16. Suriya kuma abokiyar cinikinki ce saboda yawan kayan cinikinki. Sun sayi kayan cinikinki, da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.
17. Mutanen Yahuza da na ƙasar Isra'ila abokan cinikinki ne. Sun sayi kayan cinikinki da alkama, da zaitun, da 'ya'yan ɓaure, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.
18. Dimashƙu kuma ta zama abokiyar cinikinki saboda yawan kayan cinikinki da yawan dukiyarki. Ta sayi kayanki da ruwan inabin Helbon, da farin ulu.
19. Mutanen Dan, da Yawan, da ulu suka sayi kayanki, wato gyararren ƙarfe da kayan yaji.
20. Dedan ta sayi kayanki da kayan dawakai.
21. Mutanen Arabiya da shugabannin Kedar sun sayi kayanki da 'yan raguna, da raguna, da awaki.
22. 'Yan kasuwar Sheba da Ra'ama sun sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri iri, da duwatsu masu daraja iri iri, da zinariya.