13. domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Edom. Zan kashe mutanenta da dabbobinta, zan maishe ta kufai. Za a kashe su da takobi, tun daga Teman har zuwa Dedan.
14. Mutanen Isra'la za su ɗaukar mini fansa a kan Edom. Za su aukar da fushina da hasalata a kan Edom, sa'an nan Edom za ta san sakayyata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”
15. Ubangiji Allah ya ce, “Tun da yake Filistiyawa sun yi sakayya, sun ɗauki fansa da muguwar zuciya da ƙiyayya marar ƙarewa, don su hallakar,
16. domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta Filistiyawa. Zan kashe Keretiyawa, in hallaka sauran mazaunan gāɓar teku.
17. Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na ɗauki fansa a kansu.”