1. A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2. “Ɗan mutum, ka rubuta sunan wannan rana. Ranar ke nan da Sarkin Babila ya kewaye Urushalima da yaƙi.
3. Ka yi wa 'yan tawayen nan magana da misali, ka faɗa musu cewa, ni Ubangiji na ce,‘Ka ɗora tukunya, ka ɗora ta a wuta,Ka cika ta da ruwa.
4. Ka zuba gunduwoyin nama a ciki,Dukan gunduwoyi masu kyau, wato cinya da kafaɗa,Ka cika ta da tantakwashi.
5. Ka kama mafi kyau daga cikin garken,Ka sa sauran ƙasusuwa a ƙarƙashinsa,Ka tafasa gunduwoyin,Ka kuma tafasa tantakwashin.’