41. Kun zauna a gado mai daraja, da tebur a shirye a gabansa. A kansa kuka ajiye turarena da maina.
42. A wurinta akwai hayaniyar taron mutane marasa kula, sai kuma aka kawo mutane irinsu, mashaya daga jeji. Suka sa mundaye a hannuwan matan, suka kuma sa kambi masu kyau a kawunansu.
43. Sai na yi magana a kanta, ita wadda ta ƙare ƙarfinta da yin zina, yanzu za su yi zina da ita da ta zama haka?
44. Suka shiga wurinta kamar yadda akan shiga wurin karuwa. Haka kuwa suka shiga wurin Ohola da Oholiba don su yi zina da su.
45. Amma adalai za su yanka musu hukunci irin wanda akan yi wa mata mazinata, da mata masu kisankai, gama su mazinata ne masu kisankai.