1. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
2. “Kai ɗan mutum, za ka shara'anta? Za ka shara'anta birni mai kisankai? To, sai ka faɗa masa dukan ayyukansa na banƙyama.
3. Sai ka ce masa, ‘Ni Ubangiji Allah na ce, birnin da yake kisankai, yana kuma bauta wa gumaka don ya ƙazantar da kansa, lokacinsa zai yi!
4. Ka yi laifi saboda ka zubar da jini, ka ƙazantar da kanka da gumakan da ka yi. Saboda haka ka matso da lokacinka kusa, ƙayyadaddun shekarunka sun cika. Domin haka na maishe ka abin zargi ga sauran al'umma, da abin ba'a ga dukan ƙasashe.
5. Waɗanda suke kusa, da waɗanda suke nesa za su yi maka ba'a, gama kai shahararren mugu ne, cike da hargitsi.
6. Ga shi, kowane shugaban Isra'ila da yake cikinka ya himmantu ga zub da jini bisa ga ikonsa.
7. A cikinka ana raina mahaifi da mahaifiya, ana kuma tsananta wa baƙo, ana cin zalin marayu, da gwauruwa, wato wadda mijinta ya mutu.
8. Ka raina tsarkakan abubuwa, ka kuma ɓata ranar Asabar ɗina.
9. Akwai mutane a cikinka waɗanda suke haddasa rikici don su zubar da jini, akwai kuma mutanen da suke cin abinci a matsafai, akwai mutanen da suke aikata lalata.
10. A cikinka, mutane suna kwana da matan mahaifansu, waɗansu suna kwana da mata a lokacin hailarsu.
11. Wani yakan yi lalata da matar maƙwabcinsa, wani kuma ya kwana da matar ɗansa, wani ya kwana da 'yar'uwarsa, wato 'yar mahaifinsa.
12. A cikinka mutane suka karɓi toshi don su zub da jini. Kana ba da rance da ruwa da ƙari, kana kuma cin riba a kan maƙwabcinka saboda cutar da kake yi masa, ka kuwa manta da ni, ni Ubangiji na faɗa.
13. “‘Ga shi, na tafa hannuna saboda ƙazamar riba da ka ci, da jinin da ka zubar.
14. Zuciyarka za ta iya ɗaurewa, hannuwanka kuma za su ƙarfafa a ranar da zan gamu da kai? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.
15. Zan watsar da kai cikin al'ummai, in warwatsa ka cikin ƙasashe, zan kawo ƙarshen mugayen ayyukanka.