13. Gama ba don jarraba shi ba ne, sai me kuma idan ka raina sandan? Ni Ubangiji na faɗa.
14. “Domin haka, ya kai ɗan mutum, ka yi annabci, ka tafa hannuwanka, ka kaɗa takobi sau biyu, har sau uku. Takobin zai kashe waɗanda za a kashe. Takobi ne na yin kashe-kashe mai yawa. Zai kewaye su.
15. Zai sa zukatansu su narke, da yawa kuma su fāɗi a ƙofofinsu. Na ba da takobi mai walƙiya. An yi shi kamar walƙiya, an wasa shi don kashe-kashe.
16. Ka yi sara dama da hagu, duk inda ka juya.
17. Ni kuma zan tafa hannuwana, zan aukar da fushina, ni Ubangiji na faɗa.”
18. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,
19. “Ya ɗan mutum, ka nuna hanya biyu inda takobin Sarkin Babila zai bi. Dukansu biyu za su fito daga ƙasa ɗaya. Ka kafa shaidar hanya a kan magamin hanya zuwa birni.
20. Ka nuna wa takobin hanya zuwa Rabba ta Ammonawa, da hanya zuwa Yahuza, da Urushalima, birni mai garu.
21. Gama Sarkin Babila yana tsaye a mararrabar hanya, inda hanyar ta rabu biyu, yana yin dūbā, yana girgiza kibau, yana neman shawara wurin kan gida, yana dūbān hanta.
22. A hannun damansa, dūbā yana nuna abin da zai sami Urushalima. Zai kafa mata dundurusai, a yi kururuwar yaƙi, a rurrushe ƙofofinta da dundurusai, a gina mahaurai, a kuma gina hasumiyar yaƙi.
23. Amma a gare su dūbān nan ba gaskiya ba ce, gama sun riga sun yi rantsuwa mai nauyi, amma zai tuna musu da laifinsu, don a kama su.
24. Domin haka ni Ubangiji Allah na ce, tun da yake kun sa a tuna da laifofinku, an kuma tone su, laifofinku kuma sun bayyana cikin ayyukanku, kun tonu, to, za a kama ku a cikinsu.