Ez 20:2-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ubangiji kuwa ya yi magana da ni ya ce,

3. “Ɗan mutum, ka faɗa wa dattawan Isra'ila cewa, ‘Ni Ubangiji Allah na ce kun zo ku yi roƙo a wurina, amma hakika, ba na roƙuwa a gare ku.’

4. “Za ka shara'anta su? Ɗan mutum, shara'anta su. To, sai ka sanar da su abubuwa masu banƙyama waɗanda kakanninsu suka yi.

5. Ka ce musu, ni Ubangiji Allah, na ce a ranar da na zaɓi Isra'ila na ta da hannuna, na rantse wa zuriyar Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su a ƙasar Masar, cewa ni ne Ubangiji Allahnsu,

6. a ran nan na rantse musu, cewa zan fito da su daga ƙasar Masar, zuwa wata ƙasa wadda na samo musu, ƙasar da take da yalwar albarka, wato ƙasa mai albarka duka.

7. Sai na ce musu, ‘Bari kowane ɗayanku ya yi watsi da abubuwan banƙyama da kuke jin daɗinsu, kada ku ƙazantar da kanku da gumakan Masarawa, gama ni ne Ubangiji Allahnku.’

8. Amma suka tayar mini, ba su ji ni ba, ba su yi watsi da abubuwan banƙyama da suke jin daɗinsu ba, ba su rabu da gumakan Masarawa ba. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar musu da fushina a ƙasar Masar.

9. Amma saboda sunana ban yi wannan ba, domin kada a saɓi sunana cikin sauran al'umma inda mutanen Isra'ila suke zaune, gama na sanar da kaina ga mutanen Isra'ila, a gaban sauran al'umma kuma, sa'ad da na fito da mutanen Isra'ila, daga ƙasar Masar.

10. “Sai na fisshe su daga ƙasar Masar, na kawo su cikin jeji.

11. Na ba su dokokina da ka'idodina, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu.

Ez 20