15. bai ci abinci a ɗakin tsafi ba, bai bauta wa gumakan mutanen gidan Isra'ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba,
16. bai ci zalin kowa ba, bai karɓi jingina ba, bai yi ƙwace ba, amma yana ba mayunwaci abinci, yana ba huntu tufa,
17. yana hana hannunsa aikata mugunta, bai ba da bashi da ruwa ko wani ƙari ba, yana kiyaye ka'idodina, yana kuma bin dokokina, ba zai mutu saboda laifin mahaifinsa ba, amma zai rayu.
18. Amma mahaifinsa, da yake ya yi zalunci, ya yi wa ɗan'uwansa ƙwace ya aikata mugun abu a cikin mutanensa, zai mutu saboda muguntarsa.
19. “Za ku yi tambaya cewa, ‘Me ya sa ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba?’ Sa'ad da ɗan ya bi shari'a, ya yi abin da yake daidai, ya kiyaye dokokina sosai, lalle zai rayu.
20. Wanda ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba, mahaifi kuma ba zai ɗauki hakkin laifin ɗansa ba. Adalcin adali nasa ne, muguntar mugu kuma tasa ce.
21. “Amma idan mugu ya bar dukan muguntarsa da ya aikata, ya kiyaye dokokina, ya bi shari'a, ya yi abin da yake daidai, zai rayu, ba zai mutu ba.
22. Ba za a bi hakkin laifin da ya aikata ba. Zai rayu saboda adalcin da ya yi.
23. Ni Ubangiji Allah, na ce, ina jin daɗin mutuwar mugu ne? Ban fi so ya bar mugun halinsa ya rayu ba?
24. “Amma idan adali ya bar yin adalci, ya aikata mugunta, ya yi abubuwa masu banƙyama waɗanda mugu yake aikatawa, zai rayu? Ayyukansa na adalci waɗanda ya aikata, ba za a tuna da su ba, faufau. Zai mutu saboda rashin amincin da ya yi da laifin da ya aikata.
25. “Amma kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ku ji ya ku mutanen Isra'ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba?
26. Sa'ad da adali ya bar adalcinsa, ya kuwa aikata mugunta zai mutu saboda muguntarsa.
27. Idan kuma mugu ya bar muguntarsa da yake yi, ya kuwa bi shari'a, ya yi abin da yake daidai, zai rayu.
28. Domin ya yi tunani, ya bar laifofin da ya aikata, zai rayu, ba zai mutu ba.
29. Amma mutanen Isra'ila suna cewa hanyar Ubangiji ba daidai ba ce. Ya mutanen Isra'ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba?