1. Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,
2. “Ya ɗan mutum, ka yi annabci a kan annabawan Isra'ila. Ka yi annabci a kan waɗanda suke annabci bisa ga ra'ayin kansu, ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji!’
3. “Ubangiji Allah ya ce kaito ga wawayen annabawa waɗanda suke bin ra'ayin zuciyarsu, ba su kuwa ga wani wahayi ba.
4. Ya Isra'ila, annabawanki suna kamar diloli a kufai.
5. Ba ku ƙaura zuwa inda garu ya tsage ba, ba ku gina wa mutanen Isra'ila garu don su kāre kansu a lokacin yaƙi, a ranar Ubangiji ba.
6. Suna faɗar ƙarya, suna kuma yin duban ƙarya, suna cewa, ‘Ubangiji ya ce,’ alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba, duk da haka sun sa zuciya ga cikawar maganarsu.