Esta 1:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Aka yi ta sha bisa ga doka, ba wanda aka matsa masa, gama sarki ya umarci fādawansa su yi wa kowa yadda yake so.

9. Sarauniya Bashti kuma ta yi wa mata babban biki a fādar sarki Ahasurus.

10. A rana ta bakwai sa'ad da zuciyar sarki take murna saboda ruwan inabi, sai ya umarta bābāninsa guda bakwai, waɗanda suke yi masa hidima, wato Mehuman, da Bizta, da Harbona, da Bigta, da Abagta, da Zetar, da Karkas,

11. su kirawo sarauniya Bashti ta zo wurinsa da kambin sarauta, don ya nuna wa jama'a da shugabanni kyanta, gama ita kyakkyawa ce.

12. Amma sarauniya Bashti ta ƙi zuwa kamar yadda sarki ya umarci bābānin su faɗa mata. Wannan ya sa sarki ya husata ƙwarai.

Esta 1