12. Sai suka taho wurin sarki, suka yi magana a kan dokar sarki, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ashe, ba ka sa hannu a dokar ba, cewa cikin kwana talatin nan gaba kada kowa ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, sai a jefa shi a kogon zakoki?”Sai sarki ya amsa, ya ce, “Dokar tabbatacciya ce, gama dokar Mediya da Farisa, ba ta sokuwa.”
13. Sa'an nan suka amsa wa sarki cewa, “Ya sarki, Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga ƙasar Yahuza, bai kula da kai ba, balle fa dokar da ka kafa, amma yana ta yin addu'a sau uku kowace rana.”
14. Sa'ad da sarki ya ji wannan magana, sai ransa ya ɓaci ƙwarai, sai ya shiga tunani ta yadda zai yi ya kuɓutar da Daniyel. Ya yi ta fama har faɗuwar rana yadda zai yi ya kuɓutar da shi.
15. Sai waɗannan mutane suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ka sani fa ya sarki, doka ce ta Mediya da Farisa, cewa ba dama a soke doka ko umarni wanda sarki ya kafa.”
16. Sarki kuwa ya umarta a kawo Daniyel, a tura shi cikin kogon zakoki. Sarki kuma ya ce wa Daniyel, “Ina fata Allahn nan wanda kake bauta masa kullum zai cece ka.”
17. Sai aka kawo dutse aka rufe bakin kogon, sarki kuwa ya hatimce shi da hatiminsa, da hatimin fādawansa, don kada a sāke kome game da Daniyel.