Dan 11:28-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. “Sarkin arewa zai koma gida da dukiya mai ɗumbun yawa. Zuciyarsa za ta yi gāba da tsattsarkan alkawari. Zai yi yadda ya ga dama sa'an nan ya koma ƙasarsa.

29. “A ƙayyadadden lokaci kuma zai koma kudu, amma a wannan karo abin ba zai zama kamar dā ba,

30. gama jiragen ruwa na Kittim za su tasar masa, shi kuwa zai ji tsoro, ya janye.“Zai koma ya huce fushinsa a kan tsattsarkan alkawari. Zai kula da waɗanda suka yi banza da tsattsarkan alkawarin.

31. Sojojinsa za su ɓata tsattsarkan wuri da kagararsa. Za su kuma hana yin hadayu na yau da kullum, su kafa abin banƙyama da suke lalatarwa.

32. Waɗanda suka ta da alkawarin kuma, sarki zai ƙara dulmuyar da su ta wurin daɗin bakinsa. Amma waɗanda suka san Allahnsu za su tsaya da ƙarfi su yi wani abu.

33. Waɗansu daga cikin mutane waɗanda suke da hikima, za su wayar da kan mutane da yawa. Amma duk da haka za a kashe su da takobi, waɗansu da wuta, a washe waɗansu a kai su bauta.

34. Sa'ad da suka fāɗi ba za su sami wani taimakon kirki ba, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci.

35. Waɗanda suke da hikima, za a kāshe su, don a tsabtace su, a tsarkake su, su yi tsab tsab, har matuƙar da aka ƙayyade ta yi.

36. “Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.

Dan 11