27. Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna.
28. “Sarkin arewa zai koma gida da dukiya mai ɗumbun yawa. Zuciyarsa za ta yi gāba da tsattsarkan alkawari. Zai yi yadda ya ga dama sa'an nan ya koma ƙasarsa.
29. “A ƙayyadadden lokaci kuma zai koma kudu, amma a wannan karo abin ba zai zama kamar dā ba,
30. gama jiragen ruwa na Kittim za su tasar masa, shi kuwa zai ji tsoro, ya janye.“Zai koma ya huce fushinsa a kan tsattsarkan alkawari. Zai kula da waɗanda suka yi banza da tsattsarkan alkawarin.
31. Sojojinsa za su ɓata tsattsarkan wuri da kagararsa. Za su kuma hana yin hadayu na yau da kullum, su kafa abin banƙyama da suke lalatarwa.