9. In aka zuba ruwa, sai ya toho kamar sabon tsiro.
10. Amma ɗan mutum ya mutu, ƙarshensa ke nan,Ya mutu, a ina yake a lokacin nan?
11. “Mai yiwuwa ne koguna za su daina gudu,Har tekuna kuma su ƙafe.
12. Amma matattu ba za su tashi ba daɗai,Ba za su ƙara tashi ba sam, muddin sararin sama na nan.Sam, ba za a dame su cikin barcinsu ba.
13. “Ya Allah, da ma a ce ka ɓoye ni a lahira,Ka bar ni a ɓoye, har fushinka ya huce,Sa'an nan ka sa lokacin da za ka tuna da ni!