Amos 9:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce,“Bugi ginshiƙan Haikali don shirayiduka yă girgiza.Farfasa su, su fāɗi a kan mutane!Sauran mutane kuwa,Zan kashe su a wurin yaƙi.Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.

2. Ko da za su nutsa zuwa lahira,Zan kama su.Ko sun hau Sama,Zan turo su.

3. Ko da za su hau su ɓuya a bisaƙwanƙolin Dutsen Karmel,Zan neme su in cafko su.Ko da za su ɓuya mini a ƙarƙashinteku,Sai in sa dodon ruwa yă yayyage su.

4. Idan kuwa abokan gābansu ne sukakama su,In umarce su su hallaka su datakobi,Tun da na yi ƙudurin ƙare su.”

5. Ubangiji Allah Mai RundunaYa taɓi duniya, ta girgiza.Duk waɗanda suke zaune cikintaSuna baƙin ciki.Duniya duka takan hauTa kuma gangara kamar ruwanKogin Nilu.

Amos 9