1. Ubangiji ya nuna mini wahayi, sai na ga kwandon ɓaure na ci.
2. Sai Ubangiji ya ce, “Amos, me ka gani?”Na ce, “Kwandon ɓaure na ci.”Ubangiji kuma ya ce mini, “Ƙarshen jama'ata Isra'ila ya zo. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba.
3. Waƙoƙin da akan raira a fāda, za su zama na makoki a wannan rana. Za a iske gawawwaki ko'ina. Ba za a ji motsin kome ba.”