Amos 3:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Jama'ar Isra'ila, ku kasa kunne ga wannan saƙo da Ubangiji ya aiko muku, ya ce, “Na fitar da iyalanku duka daga Masar.

2. Daga cikin dukan al'umman da nakeƙauna a duniya,Ku kaɗai ne na sani,Nake kuma kulawa da ku,Don haka zan hukunta ku sabodazunubanku.”

3. Zai yiwu a ce mutum biyu za su yitafiya tare,Amma su rasa shirya magana?

4. Zai yiwu zaki yă yi ruri a jejiBa tare da ya kama nama ba?Zai yiwu sagarin zaki yă yi gurnani akogonsaIn bai kama wani abu ba?

5. Zai yiwu tsuntsu ya fāɗi ƙasaIn ba a kafa masa tarko ba?Zai yiwu tarko ya zarguIn bai kama wani abu ne ba?

Amos 3