9. “Amma ga shi, saboda ku nahallakar da Amoriyawa,Dogayen mutanen nan masu kamada itatuwan al'ul,Ƙarfafa kuma kamar itatuwan oak,Na hallaka su ƙaƙaf.
10. Na fito da ku, wato jama'ata dagaMasar.Na bi da ku cikin jeji shekaraarba'in,Na kuwa ba ku ƙasar Amoriyawa tazama taku.
11. Na zaɓi waɗansu daga cikin'ya'yanku su zama annabawa,Waɗansu kuma daga cikin samarinkusu zama keɓaɓɓu.Ko ba haka ba ne, ya kuIsra'ilawa?Ni, Ubangiji, na yi magana.
12. Amma kun sa keɓaɓɓu shan ruwaninabi,Kuka kuma umarci annabawa kadasu isar da saƙona.
13. Zan danƙare ku a inda kukeKamar yadda ake danƙareamalanke da kayan tsaba.
14. Ko masu saurin gudu ma ba za sutsere ba,Ƙarfafa za su zama kumamai,Sojoji kuma ba za su iya ceton kansuba.