20. Nan da nan ya fara wa'azin Yesu a majami'unsu, cewa shi ne Ɗan Allah.
21. Duk waɗanda suka ji shi, suka yi ta al'ajabi, suka ce, “Ashe, ba wannan ne ya watsa masu yin addu'a da sunan nan a Urushalima ba? Ya zo nan ne ma da niyyar ya kai su gaban manyan firistoci a ɗaure.”
22. Sai Shawulu ya ƙara ƙarfafa, yana ta dama hankalin Yahudawan da suke zaune a Dimashƙu, yana tabbatarwa, cewa Yesu shi ne Almasihu.
23. Bayan an ɗan daɗe Yahudawa suka ƙulla shawara su kashe shi.
24. Amma Shawulu ya sami labarin makircinsu. Dare da rana suna fako a ƙofofin gari don su kashe shi,
25. amma da daddare almajiransa suka tafi da shi, suka zura shi ta wata taga a jikin garu cikin babban kwando.