A.m. 25:12-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Bayan da Festas ya yi shawara da majalisa, sai ya amsa ya ce, “To, ka nema a ɗaukaka ƙararka gaban Kaisar! Gun Kaisar kuwa za ka tafi.”

13. Bayan 'yan kwanaki sai sarki Agaribas da Barniki, suka zo Kaisariya don su yi wa Festas maraba.

14. Da yake kuma sun yi kwanaki da dama a can, sai Festas ya rattaba wa sarki labarin Bulus, ya ce, “Akwai wani mutumin da Filikus ya bari a ɗaure,

15. wanda sa'ad da nake Urushalima manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka kawo mini ƙararsa, suka roƙe ni in yi masa hukunci.

16. Ni kuwa na amsa musu na ce, ba al'adar Romawa ba ce a yi wa wani hukunci, don faranta wa wani rai, ba tare da masu ƙarar, da wanda aka kai ƙara, sun kwanta a gaban shari'a ba, ya kuma sami damar kawo hanzarinsa game da ƙarar da aka tāsar.

17. Saboda haka, da suka zo nan tare, ban yi wani jinkiri ba, sai kawai na hau gadon shari'a kashegari, na kuma yi umarni a kawo mutumin.

18. Da masu ƙarar suka tashi tsaye, ba su kawo wata mummunar ƙara yadda na zata a game da shi ba,

19. sai dai waɗansu maganganu da suka ɗora masa a game da addininsu, da kuma wani, wai shi Yesu, wanda ya mutu, amma Bulus ya tsaya a kan, wai yana da rai.

20. Ni kuwa da na rasa yadda zan bincika waɗannan abubuwa, sai na tambayi Bulus ko ya yarda ya je Urushalima a yi masa shari'a a can a kan waɗannan abubuwa.

A.m. 25