28. suna ihu suna cewa, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku taimaka! Ga mutumin da yake bi ko'ina yana koya wa mutane su raina jama'armu da Shari'a, da kuma wannan wuri. Banda haka kuma har ma ya kawo al'ummai a cikin Haikalin, ya ƙazantar da wurin nan tsattsarka.”
29. Don dā ma can sun ga Tarofimas Ba'afise tare da shi a cikin gari, sun kuma zaci Bulus ya kawo shi Haikalin.
30. Sai duk garin ya ruɗe, jama'a suka ɗungumo a guje suka danƙe Bulus, suka ja shi waje daga Haikalin, nan da nan kuma aka rufe ƙofofi.
31. Suna neman kashe shi ke nan, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar yaƙi, wai Urushalima duk ta hargitse.
32. A nan tāke ya ɗibi soja da jarumawa, suka ruga zuwa wajensu. Su kuwa da ganin shugaban da soja suka daina dūkan Bulus.
33. Sai shugaban ya matsa kusa ya kama Bulus, ya yi umarni a ɗaure shi da sarƙa biyu, sa'an nan ya tambaya ko shi wane ne, da abin da kuma ya yi.