2 Tar 5:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sai dukan mutanen Isra'ila suka hallara a gaban sarki, a wurin bikin, a wata na bakwai ke nan.

4. Sa'an nan dukan dattawan Isra'ila suka zo, Lawiyawa kuwa suka ɗauko akwatin.

5. Suka kuma kawo akwatin, da alfarwa ta taruwa, da dukan tsarkakakkun kayayyakin da suke cikin alfarwar. Lawiyawa da firistoci ne suka kawo su.

6. Sarki Sulemanu da dukan taron mutanen Isra'ila waɗanda suka hallara a gaban akwatin suka yi ta miƙa hadayun tumaki da bijimai masu yawan gaske, har ba su ƙidayuwa.

7. Sa'an nan firistoci suka shigar da akwatin alkawari na Ubangiji a wurinsa, wato a Wuri Mafi Tsarki na cikin Haikalin, a ƙarƙashin fikafikan kerubobi.

8. Gama kerubobin sun miƙe fikafikansu bisa a daidai wurin da akwatin yake, wato kerubobin sun yi wa akwatin da sandunansa kamar rumfa ke nan.

2 Tar 5