6. A biranen Manassa, da na Ifraimu, da na Saminu, har zuwa Naftali, a kangwayensu kewaye da su,
7. ya farfashe bagadai, ya buge Ashtarot da siffofi, ya maishe su gari, ya tumɓuke dukan bagadan ƙona turare a dukan ƙasar Isra'ila, sa'an nan ya koma Urushalima.
8. A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, bayan da ya gama tsarkake ƙasar, da Haikalin, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, da Ma'aseya mai mulkin birnin, da Yowa ɗan Yowahaz, wanda suke magatakarda domin su gyara Haikalin Ubangiji Allahnsa.
9. Sai suka zo wurin Hilkiya babban firist, suka ba shi kuɗin da aka kawo a Haikalin Allah, wanda Lawiyawa, masu tsaron ƙofa, suka tattara daga mutanen Manassa da na Ifraimu, daga sauran Isra'ila, da kuma na dukan Yahuza da Biliyaminu, tare da na mazaunan Urushalima.
10. Sai suka ba da kuɗin ga ma'aikata masu lura da Haikalin Ubangiji, da ma'aikatan da suke aiki a Haikalin Ubangiji, don gyare-gyare, su maishe shi kamar yadda yake dā,
11. sai suka ba masassaƙa da magina kuɗin, don su sayi sassaƙaƙƙun duwatsu, da katako, don yin tsaiko da tankar gine-ginen da sarakunan Yahuza suka bari, har suka lalace.