7. Kada fa ku zama kamar kakanninku ko 'yan'uwanku, marasa bangaskiya ga Ubangiji Allah na kakanninsu, saboda haka ya maishe su kufai kamar yadda kuka gani.
8. Kada ku yi taurin kai kamar yadda kakanninku suka yi, amma ku miƙa kanku ga Ubangiji, ku zo Wuri Mai Tsarki, wanda ya tsarkake har abada, ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da ku.
9. Gama idan kun juyo zuwa ga Ubangiji, 'yan'uwanku da 'ya'yanku za su sami rahamar waɗanda suka kama su, su komo wannan ƙasa. Gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne, mai jinƙai, ba zai kawar da fuskarsa daga gare ku ba, idan kun komo gare shi.”
10. Manzannin fa suka tafi gari gari a ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, har zuwa Zabaluna, amma suka yi musu dariyar raini, suka yi musu ba'a.
11. Sai mutane kaɗan na Ashiru, da na Manassa, da na Zabaluna suka yi tawali'u, suka zo Urushalima.
12. Ikon Allah kuma yana kan Yahuza, ya ba su zuciya ɗaya ta su yi abin da sarki da sarakunansa suka umarta bisa ga maganar Ubangiji.
13. Mutane da yawa kuwa suka zo Urushalima don su yi idin abinci marar yisti a wata na biyu, aka yi babban taro.