2 Tar 29:23-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Sa'an nan suka kawo wa sarki da taron jama'a bunsuran yin hadaya domin zunubi, suka ɗora hannuwansu a kan bunsuran.

24. Sai firistocin suka yanka su suka tsarkake bagaden da jinin bunsuran, don a yi kafara saboda dukan Isra'ila. Gama sarki ya umarta a yi hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi saboda dukan Isra'ila.

25. Sai ya zaunar da Lawiyawa a Haikalin Ubangiji, masu kuge, da molaye, da garayu, bisa ga umarnin Dawuda, da na Gad, maigani na sarki, da na annabi Natan. Gama umarnin daga wurin Ubangiji ya zo ta wurin annabawansa.

26. Lawiyawa suka tsaya da kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Dawuda, firistoci kuwa suna riƙe da ƙahoni.

27. Sai Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawar a bisa bagaden. Sa'ad da aka fara miƙa hadaya ta ƙonawa, sai aka fara raira waƙa ga Ubangiji, aka busa ƙaho, sai sauran masu kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushe na Dawuda, Sarkin Isra'ila, suka kama.

2 Tar 29