13. Suka ce musu, “Kada ku shigo nan da waɗanda kuka kamo daga wurin yaƙin, gama so kuke ku jawo mana laifi a gaban Ubangiji, a kan manyan zunuban da muka riga muka yi, gama Ubangiji yana fushi da Isra'ila ƙwarai.”
14. Don haka sai sojoji suka bar waɗanda suka kamo daga wurin yaƙi, da ganima a gaban sarakuna da dukan taron.
15. Sai mutanen da aka kira sunansu suka tashi, suka ɗauki kamammun, da ganimar, suka sa wa dukan waɗanda suke tsirara sutura. Suka sa musu sutura, suka ba su takalma, suka ba su abinci da abin sha, suka shafa musu mai. Suka hawar da dukan raunana a kan jakuna, suka kai su wurin 'yan'uwansu a Yariko, wato birnin itatuwan dabino, sa'an nan suka koma Samariya.
16. A wannan lokaci kuwa sarki Ahaz ya nemi taimako wurin sarakunan Assuriya.
17. Gama Edomawa suka sāke kai wa Yahuza yaƙi, suka kama mutane suka tafi da su.