2 Tar 27:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ya gina ƙofar bisa, ta Haikalin Ubangiji, ya yi gine-gine masu yawa a garun Ofel.

4. Ya kuma gina birane a ƙasar tuddai ta Yahuza, da kagara, da hasumiya a tuddai masu kuramu.

5. Ya yi yaƙi da Sarkin Ammonawa, ya kuwa ci nasara, har Ammonawa suka ba shi talanti ɗari na azurfa a wannan shekara, da alkama mudu dubu goma (10,000) da sha'ir mudu dubu goma (10,000). Haka Ammonawa suka yi ta biya a shekara ta biyu da ta uku.

6. Yotam ya shahara, saboda ya daidaita al'amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa.

7. Sauran ayyukan Yotam, da dukan yaƙe-yaƙensa da al'amuransa, an rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila da na Yahuza.

8. Ya ci sarauta, yana da shekara ashirin da biyar, ya kuma yi shekara goma sha shida yana mulki a Urushalima.

2 Tar 27