1. Yowash yana da shekara bakwai sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi shekara arba'in yana mulki a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Zibiya, daga Biyer-sheba.
2. Yowash ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji a dukan zamanin Yehoyada firist.
3. Sai Yehoyada ya auro masa mata biyu, ya haifi 'ya'ya mata da maza.
4. Bayan wannan sai Yowash ya yi niyya ya gyara Haikalin Ubangiji.
5. Sai ya tattara firistoci da Lawiyawa, ya ce musu, “Ku shiga biranen Yahuza, ku tattara kuɗi daga dukan Isra'ilawa domin a riƙa gyaran Haikalin Ubangijinku kowace shekara. Ku hanzarta al'amarin fa.” Amma Lawiyawa ba su hanzarta ba.