2 Tar 21:3-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Tsohonsu ya ba su kyautai da yawa na azurfa da zinariya, da abubuwa masu daraja, da birane masu garu a Yahuza, amma ya ba da mulkin ga Yoram, saboda shi ne ɗan fari.

4. Sa'ad da Yoram ya hau gadon sarautar tsohonsa, ya kahu sosai, sai ya karkashe dukan 'yan'uwansa da takobi, ya kuma karkashe waɗansu daga cikin sarakunan Yahuza.

5. Yoram yana da shekara talatin da biyu sa'ad da ya hau gadon sarauta, ya kuwa yi mulki a Urushalima shekara takwas.

6. Ya yi yadda sarakunan Isra'ila suka yi, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama matarsa 'yar Ahab ce. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji.

7. Duk da haka Ubangiji bai yarda ya hallaka gidan Dawuda ba, saboda alkawarin da ya riga ya yi da Dawuda, gama ya riga ya alkawarta zai ba shi haske, shi da 'ya'yansa maza har abada.

2 Tar 21