2 Tar 21:14-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. ga shi, ni Ubangiji zan aukar da babbar abboba a kan jama'arka, da 'ya'yanka maza, da matanka, da a kan abin da ka mallaka duka.

15. Kai da kanka kuma za ka kamu da ciwon hanji mai tsanani, saboda tsananin ciwo, hanjinka zai tsintsinke ya yi ta zuba kowace rana.’ ”

16. Sai Ubangiji ya kuta Filistiyawa da Larabawan da suke kusa da Habashawa, su yi gāba da Yoram.

17. Suka zo suka faɗa wa Yahuza da yaƙi. Suka washe dukan dukiyar da aka samu a gidan sarki, suka tafi da ita. Suka kuma kwashe 'ya'yansa, da matansa, ba wanda aka bar masa, sai Ahaziya autansa.

18. Bayan haka kuma, sai Ubangiji ya sa masa ciwon hanji wanda ba shi warkuwa.

2 Tar 21