7. Yanzu fa ku yi tsoron Ubangiji. Ku lura da abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu bai yarda da rashin yin adalci ba, ko son zuciya, ko karɓar rashawa.”
8. Yehoshafat kuma ya naɗa waɗansu Lawiyawa, da firistoci, da waɗansu shugabannin iyalan Isra'ilawa, saboda su yi shari'a tsakani da Ubangiji, su daidaita tsakanin masu jayayya. A Urushalima za su zauna.
9. Sai ya umarce su ya ce, “Haka za ku yi saboda tsoron Ubangiji, ku yi aminci, ku yi da zuciya ɗaya kuma.
10. A duk lokacin da 'yan'uwanku daga birane suka kawo muku maganar wata shari'a, wadda ta shafi zub da jini, ko karya shari'a, ko umarni, ko dokoki, ko farillai, sai ku koya musu, don kada su aikata laifi a gaban Ubangiji, don kada hasala ta same ku, ku da 'yan'uwanku. Abin da za ku yi ke nan, don kada ku yi laifi.