2 Tar 17:10-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Tsoron Ubangiji kuwa ya kama dukan mulkokin ƙasashen da suke kewaye da Yahuza, har ba su iya fāɗa wa Yehoshafat da yaƙi ba.

11. Sai waɗansu daga cikin Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa domin haraji. Larabawa ma suka kawo masa raguna dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700), da bunsurai dubu bakwai da ɗari bakwai (7,700).

12. Yehoshafat ya daɗa ƙasaita, ya giggina kagarai, da biranen ajiya a Yahuza.

2 Tar 17