1. Sarki Abaija kuwa ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a birnin Dawuda. Ɗansa Asa shi ya gāji gadon sarautarsa. Ƙasar ta sami sakewa har shekara goma a zamaninsa.
2. Asa ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa.
3. Ya kawar da baƙin bagadai da masujadai, ya rurrushe ginshiƙai, ya kuma tumɓuke Ashtarot.
4. Ya umarci Yahuza su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kiyaye doka, da umarni.
5. Daga cikin dukan biranen Yahuza, ya kawar da masujadai da bagadan ƙona turare. A zamaninsa an sami zaman lafiya a mulkinsa.
6. Ya giggina birane masu kagara a Yahuza, gama ƙasar tana zaman lafiya. A waɗannan shekaru bai yi yaƙi da kowa ba, saboda Ubangiji ya kawo masa salama.
7. Sai ya ce wa mutanen Yahuza, “Bari mu giggina waɗannan birane, mu kewaye su da garu, da hasumiya, da ƙofofi masu ƙyamare. Ƙasar tamu ce har yanzu, saboda mun nemi Ubangiji Allahnmu. Mun neme shi, ya kuwa ba mu salama a kowace fuska.” Suka yi ta gini, suka kuwa arzuta.