2 Sar 6:22-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Amma Elisha ya ce, “Ba za ka karkashe su ba. Ba za ka karkashe waɗanda ba kai ka kama su ta wurin takobinka ko bakanka ba. Ka ba su abinci da ruwa su ci su sha, su koma wurin shugabansu.”

23. Sai ya shirya musu babbar liyafa. Sa'ad da suka ci suka sha, sai ya sallame su, suka koma wurin shugabansu. Suriyawa kuwa ba su ƙara kai wa ƙasar Isra'ila hari ba.

24. Bayan wannan kuwa Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tattara sojojinsa duka, ya haura ya kewaye Samariya da yaƙi.

25. Aka yi yunwa mai tsanani a Samariya a lokacin da aka kewaye ta da yaƙin, har aka riƙa sayar da kan jaki a bakin shekel tamanin, an kuma sayar da rubu'in mudu na kashin kurciya a bakin shekel biyar.

26. Sa'ad da Sarkin Isra'ila yake wucewa ta kan garun birni, sai wata mace ta yi masa kuka, ta ce, “Ka yi taimako, ran sarki ya daɗe.”

27. Shi kuwa ya ce, “Idan Ubangiji bai taimake ki ba, ƙaƙa zan yi, ni in taimake ki? Ina da alkama ne ko kuwa ina da ruwan inabi?

28. Me yake damunki?”Sai ta amsa, ta ce, “Wannan mace ta ce mini, in kawo ɗana mu ci yau, gobe kuma mu ci nata.

29. Sai muka dafa ɗana muka cinye. Kashegari kuwa na ce mata ta kawo ɗanta mu ci, amma sai ta ɓoye shi.”

30. Da sarki ya ji maganar macen, sai ya keta tufafinsa, sa'ad da yake wucewa ta kan garun birni. Sai mutane suka gani, ashe, yana saye da rigar makoki a ciki.

31. Ya ce, “Allah ya yi mini hukunci mai tsanani, idan ban fille kan Elisha ɗan Shafat yau ba.”

32. Elisha kuwa yana zaune a gidansa, dattawa kuma suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki mutum, amma kafin mutumin ya isa, sai Elisha ya ce wa dattawan, “Kun ga yadda mai kisankan nan ya aiko don a fille mini kai? Idan mutumin ya zo, sai ku rufe ƙofar, ku riƙe ta da ƙarfi. Ba da jimawa ba sarki zai bi bayansa.”

33. Yana magana da su ke nan, sai sarki ya iso, ya ce, “Wannan masifa daga wurin Ubangiji ta fito, don me zan ƙara jiran Ubangiji kuma?”

2 Sar 6