2 Sar 6:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ƙungiyar annabawa da suke a hannun Elisha suka kawo masa kuka, suka ce, “Ga shi, wurin da muke zaune ya yi mana kaɗan.

2. Ka ba mu izini mu tafi Kogin Urdun, domin mu saro gumagumai a can, mu ƙara wa kanmu wurin zama.”Sai ya ce, “Ku tafi.”

3. Ɗaya daga cikinsu kuwa ya ce, “In ka yarda, ka tafi tare da mu.”Elisha kuwa ya yarda, ya ce, “To, mu tafi.”

4. Ya kuwa tafi tare da su.Sa'ad da suka isa Urdun, suka sassari itatuwa.

2 Sar 6