2 Sar 4:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Matar wani daga cikin ƙungiyar annabawa da ya rasu, ta kai kuka wurin Elisha, ta ce, “Maigidana, baranka, wato mijina, ya rasu, ka kuwa sani shi mai tsoron Ubangiji ne, amma wanda yake binsa bashi ya zo zai kwashe 'ya'yana biyu su zama bayinsa.”

2. Sai Elisha ya ce mata, “Me zan yi miki? Ki faɗa mini abin da kike da shi a gida.”Ta ce, “Ni dai ba ni da kome a cikin gidan, sai dai kurtun mai.”

3. Sa'an nan ya ce mata, “Ki tafi ki yi aron tandaye da yawa daga maƙwabtanki waɗanda ba kome a ciki.

4. Sa'an nan ki shiga ɗaki, ke da 'ya'yanki, ku rufe ƙofa. Ki ɗura mai cikin tandayen nan duka, bi da bi.”

5. Sai ta tashi daga wurinsa, ta tafi ta shiga ɗaki tare da 'ya'yanta, ta rufe ƙofar. 'Ya'yan suna kawo tandaye tana ɗurawa.

6. Da tandayen suka cika ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tandu.”Ɗan kuwa ya ce mata, “Ai, ba saura.” Sai man ya janye.

7. Sai ta koma ta faɗa wa annabi Elisha, shi kuwa ya ce mata, “Ki je ki sayar da man, ki biya bashin, abin da ya ragu kuwa ki ci, ke da 'ya'yanki.”

8. Wata rana Elisha ya wuce zuwa Shunem inda wata mace take da zama, sai ta gayyace shi cin abinci. Don haka duk lokacin da ya bi ta wannan hanya, sai ya ratsa ta gidanta, ya ci abinci.

9. Sai ta ce wa mijinta, “Na gane wannan mutum adali ne, mutumin Allah, wanda kullum yakan wuce ta hanyan nan.

2 Sar 4