1. Yosiya yana da shekara takwas sa'ad da ya ci sarauta, ya yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yedida, 'yar Adaya na Bozkat.
2. Ya yi abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji. Ya bi dukan halin kakansa, Dawuda, bai kauce dama ko hagu ba.
3. A shekara ta goma sha takwas ta sarautarsa, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, wato jikan Meshullam, magatakarda, zuwa Haikalin Ubangiji, ya ce,
4. “Ka tafi wurin Hilkiya babban firist domin a lasafta yawan kuɗin da aka kawo cikin Haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tattara daga wurin jama'a.
5. A ba da kuɗin a hannun masu lura da ma'aikata waɗanda suke gyaran Haikalin Ubangiji, su kuma su ba waɗanda suke gyaran Haikalin,
6. wato masu sassaƙa, da magina, domin a sayi katako da dutsen da aka haƙo don gyaran Haikalin.
7. Kada a tambaye su yadda suka kashe kuɗin da aka sa a hannunsu, gama su amintattu ne.”
8. Hilkiya babban firist kuwa ya ce wa Shafan magatakarda, “Na iske littafin dokoki a cikin Haikalin Ubangiji.” Hilkiya kuwa ya ba Shafan littafin, shi kuwa ya karanta shi.
9. Sai Shafan magatakarda ya tafi ya faɗa wa sarki cewa, “Baranka ya kwashe kuɗin da ya tarar a Haikali, na kuwa ba masu lura da ma'aikatan Haikalin Ubangiji.”
10. Ya kuma ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Ya kuwa karanta wa sarki littafin.