10. Iliya kuwa ya ce, “Ka roƙi abu mai wuya, duk da haka, idan ka gan ni lokacin da za a ɗauke ni, to, abin da ka roƙa za ka samu, amma idan ba ka gan ni ba, to, ba za ka samu ba ke nan.”
11. Da suka ci gaba da tafiya suna taɗi, sai ga karusar wuta da dawakan wuta suka raba su. Aka ɗauke Iliya zuwa Sama cikin guguwa.
12. Elisha kuwa ya gani, ya yi kuka yana cewa, “Ubana, ubana! Mai ikon tsaron Isra'ila! Ka tafi ke nan!” Bai kuwa ƙara ganin Iliya ba.Da baƙin ciki Elisha ya kama tufafinsa ya kece.
13. Sa'an nan ya ɗauki alkyabbar Iliya wadda ta faɗo daga wurinsa, ya tafi ya tsaya a gaɓar Kogin Urdun.
14. Sai ya ɗauki alkyabban nan da ta faɗo daga wurin Iliya, ya bugi ruwan, yana cewa, “Ina Ubangiji, Allah na Iliya?” Sa'ad da ya bugi ruwan, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, Elisha kuwa ya haye.
15. Sa'ad da annabawa hamsin da suke Yariko suka ga ya haye ya nufo su, sai suka ce, “Ai, ruhun Iliya yana kan Elisha.” Sai suka tafi su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa,
16. suka kuma ce masa, “Yanzu fa, ga mu mu hamsin ƙarfafa. Bari mu tafi mu nemo maigidanka, mai yiwuwa ne Ruhun Ubangiji ya ɗauke shi, ya jefa shi kan wani dutse, ko cikin wani kwari.”Elisha ya ce, “Kada ku tafi.”