3. Ya aikata abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi.
4. Ya kawar da wuraren tsafi na kan tuddai, ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffar Ashtoret. Ya kuma farfashe macijin tagulla wanda Musa ya yi, gama har zuwa lokacin jama'ar Isra'ila suna miƙa masa hadaya ta turaren ƙonawa. Aka ba macijin suna Nehushatan.
5. Hezekiya ya dogara ga Ubangiji Allah na Isra'ila. Ba a sami kamarsa a cikin dukan sarakunan Yahuza ba, waɗanda suka yi sarauta a gabansa, ko waɗanda suka yi bayansa.
6. Ya manne wa Ubangiji, bai bar binsa ba, ya kuma kiyaye umarnan da Ubangiji ya ba Musa.