37. Ka hana a kama ni,Ban kuwa taɓa faɗuwa ba.
38. Na runtumi abokan gābana, na kuwa hallaka su,Ban tsaya ba sai da na kore su.
39. Na fyaɗa su ƙasa, ba su iya tashi ba,Suna kwance warwar a ƙafafuna.
40. Ka ba ni ƙarfi domin yin yaƙi,Nasara kuma a kan abokan gābana.
41. Ka sa abokan gābana su gudu daga gabana,Na hallaka waɗanda suke ƙina.
42. Suka nemi taimako, amma ba wanda zai cece su,Suka yi kira ga Ubangiji, amma bai amsa musu ba.
43. Na murƙushe su, sun yi laushi kamar ƙura,Na tattake su kamar caɓi a kan tituna, na kuwa watsar da su.
44. “Ka cece ni daga jama'ata mai tawaye,Ka sa in yi mulkin al'ummai,Mutanen da ban san su ba sun zama bayina.
45. Baƙi sun zo suna rusuna mini,Sa'ad da suka ji ni suka yi mini biyayya.
46. Zuciyarsu ta karai,Suka fito daga kagararsu suna rawar jiki.
47. “Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai tsaronsa!Allah ne ƙaƙƙarfan Mai Cetona! Ku yi shelar girmansa!
48. Ya ba ni nasara a kan abokan gabana,Ya sa mutane a ƙarƙashin mulkina,
49. Ya kuɓutar da ni daga hannun maƙiya.Kai, ya Ubangiji, ka ba ni nasara a kan maƙiyana,Ka tsare ni daga mutane masu zafin hali.
50. Domin wannan zan yi yabonka cikin al'ummai,Zan raira yabbai gare ka.
51. Allah ya ba sarkinsa manya manyan nasarori,Ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shi wanda ya zaɓa,Wato ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”