2 Sam 22:14-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. “Ubangiji ya yi tsawa daga sararin samaAka kuma ji muryar Maɗaukaki.

15. Ya harharba kibau, ya warwatsa magabtansa,Da walƙiyoyin tsawa ya sa su gudu.

16. An bayyana ƙarƙashin teku a fili,An tone tussan duniya,Lokacin da Ubangiji ya yi wa abokan gāba tsautawa,Ya yi musu ruri cikin fushi.

17. Daga Sama Ubangiji ya miƙo ya ɗauke ni,Ya tsamo ni daga zurfafan ruwaye.

18. Ya kuɓutar da ni daga waɗanda suke ƙina,Daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina!

19. Sa'ad da nake cikin wahala sun auka mini,Amma Ubangiji ya kiyaye ni.

20. Ya taimake ni ya fisshe ni daga hatsari,Ya cece ni domin yana jin daɗina.

21. “Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina,Ya sa mini albarka domin ba ni da laifin kome.

22. Gama na kiyaye dokar Ubangiji,Ban yi wa Allahna tayarwa ba.

23. Na kiyaye dukan dokokinsa,Ban yi rashin biyayya ga umarnansa ba.

2 Sam 22