2 Sam 22:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan waƙa Dawuda ya raira wa Ubangiji sa'ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun Saul da dukan sauran abokan gābansa, ya ce,

2. “Ubangiji ne mai cetona,Shi ne ƙaƙƙarfar kagarata.

3. Allahna, shi ne kāriyata,Ina zaune lafiya tare da shi.Yana kāre ni kamar garkuwa,Yana tsare ni, ya kiyaye ni.Shi ne mai cetona.

4. Na yi kira ga Ubangiji,Ya cece ni daga abokan gābana.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

5. Gama raƙuman ruwa na mutuwa sun kewaye ni,Raƙuman ruwa na hallaka suna gangarawa ta kaina.

6. Mutuwa ta ɗaure ni da igiyoyinta da ƙarfi,Kabari kuma ya ɗana mini tarko.

7. A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji,Na yi kira ga Allah domin taimako.Daga cikin Haikalinsa ya ji muryata,Ya kasa kunne ga kukana na neman taimako.

8. “Sa'an nan duniya ta yi tangaɗi, ta girgiza,Harsashin sararin sama ya yi makyarkyata, ya raurawa, saboda fushin Allah.

9. Hayaƙi ya fito daga kafafen hancinsa,Harshen wuta mai cinyewa da garwashi mai ƙuna daga bakinsa.

10. Ya jā sararin sama baya ya sauko,Da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.

11. Ya hau kerub, ya tashi sama,Ya yi tafiya ta fikafikan iska.

12. Ya rufe kansa da duhu,Gizagizai masu kauri cike da ruwa suna kewaye da shi,

13. Garwashi mai ci daga tsawar walƙiya a gabansa.

14. “Ubangiji ya yi tsawa daga sararin samaAka kuma ji muryar Maɗaukaki.

15. Ya harharba kibau, ya warwatsa magabtansa,Da walƙiyoyin tsawa ya sa su gudu.

2 Sam 22