5. sai ya aiki manzanni da saƙo wurin mutanen Yabesh-gileyad ya ce, “Ubangiji ya sa muku albarka da yake kun yi wa Saul, ubangijinku, wannan alheri, har kuka binne shi.
6. Ubangiji ya nuna muku ƙaunarsa da amincinsa. Ni kuwa zan yi muku alheri saboda abin da kuka yi.
7. Yanzu sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Saul shugabanku ya rasu, mutanen Yahuza kuwa sun naɗa ni sarkinsu.”
8. Abner kuwa ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul, ya tsere da Ish-boshet, ɗan Saul, zuwa Mahanayim.
9. Ya naɗa shi Sarkin Gileyad, da Ashiru, da Yezreyel, da Ifraimu, da ƙasar Biliyaminu, da dukan Isra'ila.
10. Ish-boshet, ɗan Saul, yana da shekara arba'in sa'ad da ya ci sarautar Isra'ila, ya yi shekara biyu yana sarauta. Amma mutanen Yahuza suka bi Dawuda.
11. Dawuda ya yi shekara bakwai da rabi yana sarautar Yahuza a Hebron.
12. Abner, ɗan Ner, tare da fādawan Ish-boshet, ɗan Saul, suka tashi daga Mahanayim zuwa Gibeyon.