27. Yowab ya ce, “Na rantse da Ubangiji, hakika da ba domin ka yi magana ba, da mutanena ba za su daina runtumarka ba har gobe da safe.”
28. Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, dukan mutanensa kuwa suka tsaya, ba su ƙara runtumar mutanen Isra'ila ba, ba wanda kuma ya yaƙi wani.
29. Abner da mutanensa suka bi dare farai, suka ratsa Araba, suka haye Urdun. Suka yi ta tafiya dukan safiyan nan, suka shige Bitron, har suka kai Mahanayim.
30. Da Yowab ya komo daga runtumar Abner, ya tattara mutanensa duka, sai ya ga an rasa mutum goma sha tara daga cikin mutanen Dawuda, banda Asahel.