9. Dukan mutanen ƙasar Isra'ila suna ta jayayya, suna cewa, “Sarki Dawuda ne ya cece mu daga hannun abokan gabanmu, ya cece mu daga hannun Filistiyawa, to, ga shi, ya gudu daga ƙasar don ya tsere wa Absalom.
10. Ga shi kuma, Absalom ɗin da muka naɗa ya zama sarkinmu, an kashe shi a yaƙi. Yanzu fa, me ya sa muka yi shiru ba mu komo da sarki ba?”
11. Da labarin abin da Isra'ilawa suke cewa, ya zo gun sarki Dawuda, sai ya aika zuwa wurin firistoci, wato Zadok da Abiyata, a faɗa musu su tambayi dattawan Yahuza abin da ya sa suka zama na ƙarshe a kan komar da sarki a gidansa.
12. Ya ce, “Ai, ku 'yan'uwana ne, da ƙasusuwana, da namana. To, me ya sa za ku zama na ƙarshe a kan komar da sarki?
13. Ku ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba ƙashina da namana ba ne? Allah ya hukunta ni idan ba kai ne shugaban rundunar sojojina a maimakon Yowab ba.’ ”
14. Da haka Dawuda ya rinjayi zukatan mutanen Yahuza, suka zama ɗaya, kamar mutum guda. Sai suka aika wurin sarki, cewa, ya komo tare da dukan fādawansa.
15. Sa'ad da sarki ya iso Urdun. Mutanen Yahuza suka tafi Gilgal suka taryi sarki, domin su hawo da shi Urdun.