Da haka Dawuda ya rinjayi zukatan mutanen Yahuza, suka zama ɗaya, kamar mutum guda. Sai suka aika wurin sarki, cewa, ya komo tare da dukan fādawansa.