2 Sam 19:24-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sa'an nan Mefiboshet jikan Saul ya gangara ya taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har zuwa ranar da ya komo da nasara Mefiboshet bai wanke ƙafafunsa ba, bai kuma yi gyaran fuska ba, bai ma wanke tufafinsa ba.

25. Sa'ad da ya iso daga Urushalima don ya taryi sarki, sai sarki ya ce masa, “Me ya sa ba ka tafi tare da ni ba, Mefiboshet?”

26. Mefiboshet ya amsa ya ce, “Ya ubangijina, sarki, barana ya ruɗe ni, gama na ce masa ya yi wa jaki shimfiɗa don in hau in tafi wurin sarki, gama ka sani ni gurgu ne, ranka ya daɗe.

27. Barana ya ɓata sunana a gaban ubangijina, sarki. Amma ranka ya daɗe, ya sarki, kai kamar mala'ikan Allah kake, sai ka yi abin da ya yi maka daidai.

28. Gama dukan mutanen gidan kakana sun cancanci mutuwa a gabanka, ranka ya daɗe, amma ga shi, ka sa na zama ɗaya daga cikin waɗanda suke ci a teburinka. Ba ni da dalilin da zai sa in yi wa sarki wani kuka kuma.”

29. Sai sarki ya ce masa, “Me ya kawo wannan magana a kan harkokinka? Ai, na riga na zartar, cewa, kai da Ziba za ku raba mallakar Saul.”

30. Mefiboshet ya ce wa sarki, “A ma bar masa duka ya mallaka, ni dai tun da ubangijina, sarki, ya komo gida lafiya, to, alhamdu lillahi.”

31. Barzillai Bagileyade kuma ya gangara daga Rogelim zuwa wurin sarki domin ya yi wa sarki rakiya zuwa hayin Urdun.

2 Sam 19