2 Sam 19:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Aka faɗa wa Yowab, cewa, sarki yana kuka, yana makoki domin Absalom.

2. Saboda haka sai nasarar da aka ya a ranar ta zama makoki ga jama'a duka, gama jama'a suka ji an ce sarki yana baƙin ciki domin ɗansa.

3. Sojojin suka shiga birni sururu kamar waɗanda sukan shiga birni a ɓoye da kunya saboda sun gudu daga wurin yaƙi.

4. Sarki ya rufe fuskarsa, ya yi kuka da ƙarfi, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ya Absalom, ɗana, ɗana!”

5. Yowab kuwa ya tafi wurin sarki a gidansa ya ce, “Yau ka kunyatar da mutanenka duka waɗanda suka ceci ranka, da rayukan 'ya'yanka mata da maza, da rayukan matanka, da rayukan ƙwaraƙwaranka.

2 Sam 19