11. Dawuda kuma ya ce wa Abishai da dukan fādawansa, “Ga shi ma, ɗana na cikina yana neman raina, balle wannan mutumin Biliyaminu! Ku bar shi ya yi ta zagi, gama Ubangiji ne ya umarce shi.
12. Watakila Ubangiji zai dubi azabata, ya sāka mini da alheri saboda wannan zagin da aka yi mini yau.”
13. Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu. Shimai kuwa yana biye da su ta gefen dutse, yana tafe, yana ta zagi, yana jifarsa da duwatsu, yana masa ature.
14. Sarki da dukan jama'ar da suke tare da shi suka isa Urdun a rafke. Sai suka shaƙata.
15. Absalom kuwa ya zo Urushalima tare da dukan mutanen Isra'ila da suke tare da shi. Ahitofel kuma yana tare da shi.